Akwai korafe korafe da dama a wasu jihohin Nigeria dangane da yadda gwamnonin jam’iyyar APC da ke mulki da ma wasu na jam’iyya PDP mai adawa ke nada wadanda suke son su gajesu.
A jihohin Zamfara, Yobe da Imo dukkansu jihohin APC gwamnoninsu sun nada wadanda za su gajesu karfi da yaji saboda sun ki sauraron sauran ‘yan jam’iyyarsu dake neman tsayawa takara kamar yadda jaridar Daily Trust ta Litinin ta ruwaito.
A jihar Zamfara gwamna Abdulaziz Yari ya yi gaban kansa ya nada kwamishanan ma’aikatar kudi a matsayin wanda zai tsaya takara domin ya gajeshi. Ya yi hakan ne maimakon ya ba mataimakinsa Ibrahim Wakkala dama, wanda tun da dadewa ya nuna sha’awar tsayawa. Sauran ‘yan takaran ma ba’a batunsu. Magoya bayansa da Wakkala da wasu sun nuna fushinsu da matakin da gwamnan ya dauka. Wasu sun sha alwashin yin gaban kansu. Kuma tuni Wakkala ya sayi takardar tsayawa takarar gwamnan jiharsa.
Da alama tana kasa tana dabo saboda Sanata Kabiru Marafa ya kira ‘yan jam’iyyar da su shirya domin su yi ‘yan tinke a zaben fidda gwani na takarar ‘yan majalisar tarayya da na gwamnan da majalisar jiha. Sai dai har yanzu gwamna Yari ya dage ba za’a yi tinke ba wai domin sun tsayar da ‘yan takara ko.
A jihar Yobe ‘yan takara uku suka kushewa tsayar da Mai Mala Buni a matsayin dan takarar gwamnan da gwamna Ibrahim Geidam ya yi. Daya cikin ‘yan takaran Alhaji Sidi Yakubu Karasuwa wanda ya shugabanci kemfen din gwamnan a shekarun 2011 da 2015 ya ce shi tuni ya sayi takardar tsayawa zabe kuma ya amince a yi ‘yan tinke.
Akan tsayar da dan takara da gwamnan ya yi Alhaji Karasuwa ya ce babu ruwansa da wannan. Kazalika Alhaji Ali Kolomi wanda ya sayi takardar tsayawa zaben ya lashi takobi ba zai janyewa kowa ba. Yace baya tsoron kowa domin Allah ne yake ba da shugabanci. Abinda suke bukata shi ne a ba kowa damar tsayawa. Kada a yi anfani da wakilai a yi dauki dora”
A can jihar Imo ma bata canja zani ba inda gwamnan jihar Rochas Okorocha ya nada surikinsa, Uche Nwosu ya gejeshi. Amma mataimakin gwamnan Eze Madumere ya rantse sai ya tsaya takarar gwamnan. Kos hi ma Injiniya Chuks Ololo mijin kanwar gwamnan ya ce shi ma dashi za’a dama a takarar gwamnan. Sakataren gwamnati George Eche shi ma ya tsunduma cikin takarar.
Barrister Chima Anozie wanda shima ya sayen takardar tsayawa takara ya yi kira magoya bayansa su manta da batun yin anfani da wakilai. ‘Yan tinke za’a yok o ta halin yaya, injishi.
Tsayar da Adekunle Akinlade da gwamnan jihar Ogun Ibikunle Amosun ya yi a matsayin dan takara cikin ‘yan takara 10 ya bar kura baya. ‘Yan jihar sun yi watsi da wannan dauki dora da gwamnan yak e neman yi masu. A saboda haka kwamishanan cinikayya da masana’antu Otunba Bimbo Ashiru ya yi murabus domin ya tsaya takarar gwamna ya kalubalanci Akinlade da gwamnan ya tsayar.
Haka dai lamarin yake daga jiha zuwa jiha a duk fadin Nigeria kamar yadda jaridar Daily Trust ta ranar Talata 11 ga watan Satumba ta ruwaito
Facebook Forum