Malaman addinai a jihar Filato, sun bukaci al’uma dasu hada kai batare da nuna banbanci ba wajen bankado bata gari dake hallaka ran al’uma da basu jiba basu gabi ba.
A cikin ‘yan kwanakin nan ne dai aka samu tashin boma Masallacin da Sheikh Sani Yahaya Jingir, ke gudanar da Tafsirin Azumin Ramadan, da yayi sanadiyar rasa rayuka da dama dakuma wanda aka sa a Ikilisiyar ECWA, ta Tudun Wada wanda dan yardan Allah bai hallaka kowa ba, duk a garin Jos, ta jihar Filato.
A cewar shugaban majalisar Malamai ta kungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir, salon da maharan ke bi suna da dama domin haka yakamata Musulmi da Kirista, a hada kai domin taimakekeniya da zaman lafiya.
Shima mataimakin sakatren darikar ECWA, ta kasa Rev. Eliezer Baba, yace a matsayinsu na shugabanin addinai dam ace Allah ya basu su fadakar da mabiyansu matakan da zasu bi wajen karfafa jama’a ta yadda zasu zauna lafiya da juna.