Taimakawa Mabukata Ya Zama Babban Buri Na Bayan Kammala Karatu - Saudatu Kokoroko

A shirinmu na mata da irin rawar da suka taka a cikin al’ummarsu a yau Dandali yayi nisan kiwo, domin kuwa ya fita daga Nijeriya, zuwa kasar Ghana, inda muka samu bakuncin wata matashiya bahausa ‘yar asalin kasar Ghana.

Saudatu Nuhu Kokoroko wacce ta ce tayi karatunta duka a kasar Ghana inda ta samu shiga jami’ar ‘Central Ghana, ta bayyana mana cewa neman gurbin karatu ba wani abu ne mai wuya ba sai dai ta fuskanci matsalar rashin dora ta a kan hanyar irin karatun da dalibi ya kamata ya yi.

Bayan kammala karatun, ta samu damar aiki a wata ma’aikata mai suna Dan gaskiya – ta ce babban matsala da ta fara cin karo da ita a wajen aikin ta dai shine ta lura da cewar abinda aka koya masu a makaranta ba shi ne abinda da ta rar a wajen aiki ba.

Saudatu, ta ce lallai ta yarda akwai banbancin abinda aka koya maka a makaranta da kuma gabatar da shi a aikace, ta kara da cewa a yanzu da take girma ta tabbatar da cewa yanzu ne take sanin kanta take kuma ganin mecece rayuwa.

Malama Saudatu, ta ce a yanzu ta tabbatar da abinda ranta ke bukata da sha’awa wato taimakawa yara marayu da mata mabukata ko wadanda mazajensu suka rasu.

Your browser doesn’t support HTML5

Taimakawa Mabukata Ya Zama Babban Buri Na Bayan Kammala Karatu - Saudatu Kokoroko