Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abubakar Umar: Shugabancin Matasa Shine Mai Dorewa


Abubakar Umar
Abubakar Umar

Matasa sun farga da cewar iyayen gijinsu da gangan suka kawar da matasa, domin su ci karensu ba babbaka a harkar siyasa da tafiyar ta da cigaban kasa.

Mulkin matasa a Nijeriya ba yau farau ba, kuma matasan da suke cin karensu ba babbaka wala Allah ana tauye su ne da zarar sun hau karagar mulki, gudun kada suyi bore su kwace ragamar mulki, ko kuma matasan da suka dace basa samun dama a siyasar yanzu.

Abubukar, na ganin cewa cigaban da aka samu a wancan lokaci dukkaninsu matasa ne suka samar da su, kamar misali a lokacin da shugaba Buhari ya hau karagar mulki ya samar da cigaba lokacin yana matashi, Yakubu Gawon, Ibrahim Babangida, Janar Murtala Ramat Muhammad, dukkaninsu matasa ne, kuma dukkaninsu sun taka rawar gani da har yanzu ana ganin ayyukansu a kasa.

Abubukar, yana ganin a duk lokacin da matasa suka farga, suka kuma tabbatar da cewar su na da matsala, a sannan ne zasu magance kadan daga cikn matsalolinsu, kuma da ace matasan zasu yi taron dangi wajen kwato wa kansu 'yanci, da tuni an magance matsalolin da kasar nan take ciki.

Har ila yau ya ce suna nan suna tara matasa masu hikima domin ganin cewar an fitar da su daga kangin da suke ciki.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:14 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG