Ana iya sarrafa na’urar mutunmutumi ‘Robot’ ta wannan zamanin ko sa ta wasu ayyuka da zata gabatar cikin kankanin lokaci wanda takan yi aiki ba kakkautawa, kama ta yi aiki batare da kuskureba, ko gajiya da neman hutu.
Amma abun tambaya anan shine, wai kuwa robot na iya gabatar da aiki da kuma lura da kura-kuran sa da zummar gyara su kuwa? Kusan ana iya cewa babu wani aiki da na'urar robot bata iya yi a wannan zamanin, kama daga aikin share gida, saye da sayarwa a kasuwanni, hada motoci, da dai makamantansu, amma wani abun lura shine babu yadda zai iya gane cewar yayi kuskure balle ya koma baya don ya gyara.
Wasu masana kimiyya daga jami’ar Carnegie Mellon dake birnin Pittsburgh, a jihar Pennsylvania ta Amurka, suna gudanar da wani aiki don inganta robot, da zai iya gabatar da aiki tare da iya gane ko yayi wani abu bisa kuskure, don aiwatar da gyara cikin gaggawa.
Suna aiki don kyautata tunanin mutunmutumin ‘robot’ da zai iya gane duk wani abu da ya taba yi da kuma lura da yadda yake a da, da zummar gyara shi idan ya lura bai aiwatar da aikin yadda ya kamata ba. Za’a saka masa tunani irin na mutane, wanda zai iya tuna abubuwa da suka gabata.
Da lura da wajen da duk wani abu ya cancanta, da iya banbance dai-dai da kuskure, duk batare da an sanar da shi ba, masanan sun kara tabbatar da cewar za’a iya cinma wannan nasarar, amma aiki ne tukuru da zai dauke su lokaci, nan da shekaru kadan.
Facebook Forum