Rundunar 'yan sandan Najeriya a babban birnin tarayya Abuja ta tabbatar da mutuwar mutane uku biyo bayan wani mummunan hatsarin mota da ya auku a Dutse Baupma da ke cikin birnin na Abuja.
Rundunar ta ce a karshen mako ne ta sami kiran gaggawa daga wani dan kasa na gari game da aukuwar hadarin, inda ta tura jami'anta aka debi wadanda abin ya rutsa da su zuwa babban asibitin gwamnati da ke Kubwa.
Abin bakin ciki a cewar kakakin 'yan sandan na Abuja, SP Josephine Ade likitoci sun tabbatar da mutuwar mutane uku, wato Hosea Stephen mai shekaru talatin da hudu, Muhammad Lawal dan shekaru talatin da biyu da Bashir Shu'aib dan shekaru ashirin da biyar.
Bugu da kari, 'yan sanda sun kwashe motoci guda hudu da hatsarin ya rutsa da su, amma wata motar alfarma kirar jeep ta wani jami'in hukumar tsaron farin kaya DSS, ya gaggauta dauke ta da wata wacce ita ma na cikin wadanda suka yi hatsarin.
‘Yan sanda sun ce tuni sun kaddamar da bincike don gano musabbabin aukuwar wadannan munanana tagwayen hadurran.