ACCRA, GHANA - Da kuma matsalolin tattalin arzikin kasar gaba daya ne suka yi tasiri a shekarar 2022 da muka yi bankwana da ita a Ghana.
A wannan shekara ta 2023, mashaharta sun bayyana wa Muryar Amurka burace-buracensu ga Ghana, inda suka yi hasashen samun sauki a bangarori daban daban, fiye da shekarar da gabata.
Masani a hulda tsakanin kasa da kasa da tsaro, Irbad Ibrahim ya ce yana da burin Ghana ta kasance kasa da ta fi kowacce zaman lafiya a Afirka sannan kuma gwamnati da kamfanoni su baiwa matasa aikin yi domin dakile fitar matasa zuwa kasashen waje.
Masani a kan harkokin tsaro Adib Sani, a nasa bangaren ya ce, yana da burin a samu fahimtar juna tsakanin jami'an tsaro da jama'a da kuma hukunta duk jami'in tsaro da ya karya doka.
Masu fashin baki a kan al'amuran yau da kullum Salahuddeen Yunus Wakpenjo da Issah Mairago Gibril Abbas sun yi fatan samun karin ci gaba a bangaren tattalin arziki, siyasa da tsaro.
Sai dai masani a kan tattalin arziki, Hamza Adam Attijjany, ya ce duk da cewa akwai alamar darajar kudin Ghana za ta kara farfadowa a wannan shekarar, amma farashin kayan abinci zai iya tashi domin gwamnati za ta janye tallafin shigowa da kayan abinci daga kasashen waje da kasha 50% yadda manoman cikin gida za su samarwa kasar abinci.
Kuma yarjejeniyar da ake yi da IMF zai shafi daukar sabbin ma'aikata, wanda hakan zai kawo cikas ga tattalin arziki.
Saurari cikakken rahoto daga Idris Abdallah Bako:
Your browser doesn’t support HTML5