Ta'adancin Boko Haram ya Rike Mana Wuya

Kalubalen ta'adanci ya shafi duk kasashen dake yankin tafkin Chadi, in ji Air Marshal Alex Badeh hafsan hafsoshin sojojin Najeriya, ya furta haka ne a jawabi da yayi a toron hafsoshin kasashen dake makwabtaka da tafkin na Chadi. Saboda haka, taron, yace yana da mahimmanci.

Yace taron yana da mahimmanci domin zai duba hanyoyin da zasu hada gwiwa domin su yaki Boko Haram da kowace kungiyar ta'adancin a yakinsu da kuma tabbatar da doka da oda.

Alex Badeh yace babu mugun ta'adanci da ya rike masu wuya irin ta'adancin Boko Haram wanda ya jefa al'umma cikin mawuyacin hali da karya tattalin arziki..

Badeh ya cigaba dacewa su 'yan ta'ada babu ruwansu da iyakar kasa da kasa. Koina kutsawa suke yi. Saboda haka ya zama wajibi kasashen su hada karfi da karfe su magance matsalar.

Babban daraktan tafkin Chadi Sanusi Imrana yace taron zai ba sauran kasashen duniya damar tallafawa kasashen tafkin Chadin wajen kawo tsaro da farfado da tattalin arziki.

Masana harkokin tsaron Najeriya irinsu Rabe Nasir na mara baya wa irin wannan gamayyar da nanata matukar aka sakarwa sojoji mara da tsame son zuciya za'a iya cimma nasara a yakin.

Ga rahoton don karin bayani.