Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Manyan Masu Laifi Sun Arce Daga Gidan Yari


This photo provided by New York state governor's office shows Gov. Andrew Cuomo on a catwalk, looking into the cell that inmates escaped from at a maximum-security prison near the Canadian border in Dannemora, N.Y., June 6, 2015.
This photo provided by New York state governor's office shows Gov. Andrew Cuomo on a catwalk, looking into the cell that inmates escaped from at a maximum-security prison near the Canadian border in Dannemora, N.Y., June 6, 2015.

A safiyar jiya Asabar ne mutane biyu suka kubuce daga gidan Yari mai tsatstsauran tsaro na jihar New York, ana tsare da firsinonin biyu ne kan laifin kisan kai da aka same su da aikatawa.

Jami’an tsaro a birnin New York na amfani da jirage masu saukar ungulu da sauran abubuwan hawa, domin farautar Richard Matt mai shekaru 48 da David Sweat mai shekaru 34, ‘yan sanda sunce an gano bacewar mutane biyu ne alokacin jami’in firsin din ke sintiri da tabbatar da kowa na kwance a gadon sa da missalin karfe biyar da rabi na safe. Firsinonin sun bar rubutatcen sakon ban kwana makale a bango.

Firsinonin sun fasa bango da haka rami har zuwa wata hanya dake karkashin kasa, inji jami’an tsaro.

A tarishin gidan Yarin mai tsatstsauran tsaro babu wani da ya taba samun nasarar kubucewa tun da aka gina shi a shekara ta 1865. Sama da kwararrun ‘yan sanda 200 ne suka fantsama neman firsinonin, amma har yanzu babu wata nasara kan sanin inda suke ko inda suka nufa.

XS
SM
MD
LG