Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kujerar Gwamna Bana Masuyin Barci Bane


Gwamnan jihar Bauchi Barrister M.A Abubakar, ya sha alwashin gurfanar da duk wanda ake zargi da handamai kudaden Gwamnatin jihar, Inda ya zargi Gwamnatin da ta shude da cewa ta shantake da kuma yin cin kacha wa tattalin arzikin jihar Bauchin , da kuma barin basussuka na biliyoyin Naira.

A nashi bayanin tsohon Gwamnan jihar Bauchi Malam Isa Yuguda, yace zancen bacin ba haka bane, abin da ya sani shine cewa ya karbi bacin baki domin aikin gina filin jigin sama sauran basussukan gadon su yayi.

Dangane da batun motoci takwas da aka ce an sayarwa da matar tsohon Gwamnan sai Malam Yuguda yace “ Doka ne ka’ida ne na Gwamnati bawai wani kawai yaje yace ga kudi ba ni nayi amince da a sayarda ina Gwamna an zabe ni kuma lokaci da na ba izini ina da damar yin haka.

Amma inji wani mai sharhi akan siyasa Alhaji Shehu Musa Gaban yace kafin ya zama Gwamna yakamata yasan inda zai samu kudi domin yasan babu kudi a jihar idan bazaka iya aikin Gwamna ba kada ka nema kujerar Gwamna bana masuyi barci bane.

XS
SM
MD
LG