Wata yarinya ta yi mutuwar karya domin gudun kada saurayin ta ya kashe ta bayan sun sami 'yar rashin fahimta a tsakanin su inda saurayin da ya turo ta ta fado daga matakalar hawa bene sannan ya sa wani tsumma ya shake mata wuya, a cewar wani rahoto da 'yan sandan Amurka suka fitar ya bayyana.
Yarinyar ta dauke lunfashin ta ne ta yi kamar ta mutu domin gudun kada saurayin nata da ke rike da wuyan ida hallaka ta, shi kuma da ya taba hancin ta ya ji tabar lumfashin sai ya jefar da ita. a cewar baban jami'in 'yan sandan Chief Mark Diluzio, matar tana kwance a asibiti cikin mawuyacin hali.
An chaji Saurayin mai suna Bartholomew Palumba dan sheakaru 25, da yunkurin aikata kisan kai da kuma aikata lafin saka rayuwar yarinyar cikin hatsari. a yanzu haka dai an kai shi gidan wakafi inda kotu ta sa kudin belin sa har dalar Amurka dubu dari $ 100,000 wato kwatankacin Naira Miliyan ashirin da biyu kenan N22,000000.
A cewar jami'an tsaron, ran saurayin ya baci ne a sakamakon wani rubutaccen sako wato text message da wani ya aika mata shi kuma sai ya gani a wayar budurwar tasa.
Saurayin ya daka tsalle ne ya cafke mata wuya, sannan kuma ya yi ta dunkule hannu ya dinga jubgar ta daga karshe kuma ya tura ta kasa inda ta fado daga matakalar bene. ya rin yar dai ta rarrafa ne da kyar sanna ta kira lambar neman taimakon gaggawa, a yayin da motar ta iso sai saurayin ya tada murya ya ce "ai dama baki mutu ba".