Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abinci Mai-Gina Jiki Na Kara Fahimtar Karatu Ga Yara


BACK TO SCHOOL RETAILERS
BACK TO SCHOOL RETAILERS

A yayin da ake kokarin komawa makarantu a nan kasar Amurka, musamman yara ‘yan firamari da sakandire. Iyayen yara, sun dau alwashin ganin an ba ‘yayan su abinci mai gina jiki a makarantu.

Mujallar gidauniyar W.K. Kellogg, ta wallafa cewar iyayen yara da dama sun nuna damuwar su, dangane da irin abincin da ake ba ‘yayan su a makarantu. Sun bukaci da cewar akwai bukatar a ba ‘yayan su abinci mai gina jiki, kamar kayan marmari, ganyayyaki, a guji basu abinci wanda ke dauke da awon makamin abinci mai yawa. Don sun fahimci cewar ‘yayan su na cin abincin da ke sasu kiba mara ma’ana.

Idan ba’a mantaba a shekarar 2010 shugaban kasa Barak Obama ya rattaba hannu a wata doka, dake umurtar mahukunta a makarantu, da su bama yara abinci mai gina jiki. Wanda daga bisani, Uwar gidan shugaban kasar Micheal Obama ta dauki wanna, a matsayin shirin gangami da wayar da kan iyaye dangane da hadduran cin abinci marasa gina jiki wajen girman yara.

Masana na ganin cewar, baiwa yaran abinci mai gina jiki, zai taimaka matuka wajen kara hazaka da fahimtar yaran.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG