Stoltenberg, ya furta haka ne yau Jumnma'a da isarsa Amsterdam domin ya halarci taron ministocin tsaro na kungiyar tarayyar turai.
Yace hare haren da Rasha take kaiwa masu tsanani da jiragen yaki, sun fi auna 'yan hamayya lamarin da yake kara janyo zaman dar dar,haka kuma yayi zargin matakan na Rasha suna keta sararin samaniyar kasashe dake kungiyar tsaro ta NATO da kuma na Turkiyya.
A wani lamari kuma, an ce sojojin gwamnatin sham din wadnda suke samun goyon bayan jiragen yakin Rasha sun sake kwace wani gari dake hanun Deraa, kamar yadda aka ji a tashar talabijin ta kungiyar Hezbollah da ake kira Al-Mannar da kuma ta bakin kungyar rajin kare hakkin Bil'Adama ta Syria, a yau Jumma'a. Wannan lamari yana zuwa ne kwana daya bayan da wani taron kasa da kasa da Majalisar Dinkin Duniya ta dauki nauyin shiryawa na neman gudumawar kudi domin ayyukan jinkai ya sami alkawarin dala milyan dubu 10.