Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen yakin Syria sun kashe mutane a kauyukan dake 'yan tawaye


Jiragen yakin Syria
Jiragen yakin Syria

A Syria, 'yan gwagwarmaya suka ce hare haren da jiragen yakin kasar suka kai kan kauyuka birnin Damascuss, wadanda suke hanun 'yan tawaye, sun halaka akalla mutane ashirin.

Kungiyar da take rajin kare hakkin Bil'adama a Syria mai cibiya a Ingila, tace mata da yara suna cikin wadanda hare haren suka rutsa da su, a farmakin da dakarun gwamnatin suka kai jiya Alhamis, kan kauyen da ake kira Hammouriyeh.

Wasu da dama kuma sun jikkata.

Ahalinda ake ciki kuma,ministan harkokin wajen kasar Walid Muallem, yace a shirye kasarsa take ta shiga taron sulhu kan rikicin kasar da za'a yi a Geneva, "ba tareda shishigin kasashen waje ba,"mako daya bayan da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani shirin sulhu da kasa da kasa ke goyon baya, da zummar kawo karshen yakin basasar da kasar take fuskanta.

Ministan ya bayyana haka ne yayinda yake magana jiya Alhamis a Beijing, inda ya gana da tawakaran aikinsa na China Wang Yi. Muallim yace, tawagar gwamnati zata shirya da zarar ta sami jerin sunayen mutanen da zasu wakilci 'yan tawayen.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG