Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan adawan Syria Sun Isa Birnin Geneva


Ministan harkokin wajen Qatar Hamad Bin Jassim Al-Thani yake zantawa da sakataren kungiyar kasashen Larabawa Nabil Al-Arabi a wajen wani taro da suka yi a birnin Doha akan kasar Syria.
Ministan harkokin wajen Qatar Hamad Bin Jassim Al-Thani yake zantawa da sakataren kungiyar kasashen Larabawa Nabil Al-Arabi a wajen wani taro da suka yi a birnin Doha akan kasar Syria.

Bayan kwashe kusan shekaru biyar ana yaki basasa a kasar Syria, ana shirin wani zaman sasanta rikicin kasar a birnin Geneva, taron da ake fargabar bangaren masu shiga tsakani da Saudiya ke marawa baya ba za su halarta ba.

Tawagar hadakar 'yan adawar kasar Syria sun isa birnin Geneva domin fara tattaunawa kan yadda za a shawo kan rikicin kasar.

Sai dai babu tabbacin ko mambobin kwamitin shiga tsakanin rikicin da kasar Saudiyya ke marawa baya za su halarci taron kai-tsaye, domin kawo karshen yakin basasan na Syrian.

Wakilan Majalisar Dinkin Duniya, sun fara kaddamar da taron a jiya Juma’a, duk da kauracewa taron da mambobin kwamitin da ke shiga tsakani a rikicin, wanda Saudiyya ke goyon baya suka yi.

Taron na ranar juma’a wanda ya fara gudana a ofisoshin Majalisar Dinkin duniya da na wakilin Majalisar kan rikicin Syria Steffan De Mistura da kuma wakilan gwamnatin Syria, wadanda Ambasadan Syrian a Majalisar, Bashar Ja’afar ya jagoranta.

Bayan taron, De Mistura, ya ce yana da burin ya gana da mambobin kwamitin masu shiga tsakanin a gobe Lahadi.

XS
SM
MD
LG