Zakarun kwallon kafa na duniya Faransa sun fice daga gasar cin kofin nahiyar turai ta 2020 bayan da Switzerland ta doke ta a bugun fenarti.
Wasan ya kai ga karin lokacin bayan da aka tashi da ci 3-3 abin da ya tilasta zuwa matakin bugun fenarti.
Tun da farko masu hasashe da dama sun nuna cewa mai yi wa Faransa ce za ta lashe kofin wannan gasa.
Sai dai Switzerland ta shammace ta a wasan da kuma bugun fenarti da aka yi inda Faransa ta ci kwallaye hudu yayin da Switzerland ta ci duka biyar.
Kylian Mbappe ne ya zubarwa da Faransa bugun fenarti dinta, wanda hakan ya kawo karshen karawarta a gasar.
Switzerland ce ta fara zira kwallo a wasan, amma daga baya Karim Benzema ya farke ya kuma kara wata ta biyu cikin dan kankanin lokaci.
Faransa ta kara da ba da tazara a wasan bayan da Paul Pogba ya zira wata kwallon a minti na 75, abin da ya kai wasan 3-1, amma bayan wani kukan kura da suka yi, ‘yan wasan Switzerland sun farke duka kwallayen wadanda Haris Seferovic da Mario Gavranovic suka zira.
Hakan ya kai wasan ga karin lokaci har kuma ya kai ga bugun fenarti.
Yanzu Switzerland za ta hadu da Spain wacce ta lallasa Croatia ita ma da ci 5-3.