Belgium ta yi waje-rod da Portugal a gasar cin kofin nahiyar turai ta Euro 2020 bayan da ta zira mata kwallo daya mai ban haushi.
Portugal ita ce take rike da kofin gasar.
Dan wasan Belgium Thorgan Hazard ne ya zira kwallon kafin a je hutun rabin lokaci, abin da ya kwace ta a karawar da suka yi a zagayen ‘yan 16.
Hakan na nufin Belgium za ta hadu da Italiya kenan a ranar Asabar.
Ita dai Portugal ta yi iya bakin kokarinta da aka dawo daga hutun rabin lokaci a kokarin da ta yi na farke kwallon, amma abin ya ci tura.
Belgium ta samu nasarar ce duk da cewa kyaftin dinta Kevin De Bruyne ya fita a wasan saboda raunin da ya samu bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.
Ita ma kasar Czech Republic ta lashe wasanta bayan da ta doke Netherland da ci 2-0
A gobe za a kara tsakanin Spain da Croatia yayin da France za ta fafata da Switzerland