Shekara tara bayan da ta lashe kofin gasar zakarun nahiyar turai ta UEFA, a wannan shekara, Chelsea ta sake lashe kofin bayan da ta doke Manchester City da ci daya mai ban haushi.
‘Yan wasan na Thomas Tuchel sun samu ban iska ne a minti na 42 a lokacin da Kai Havertz ya dauki wata kwallo da aka duko daga kuryar hagu, wacce ya zura a ragar City, bayan wata ‘yar arangama da suka yi da Ederson.
An yi ta kai ruwa rana tsakanin kungiyoyin biyu wadanda dukansu daga gasar Premier ta Ingila suka fito.
Wasan ya gudana ne a filin wasa na Estadio do Dragao da ke kasar Portugal.
A mintinan farkon wasan, City ta taso da karfinta, amma yunkurowa da Chelsea ta yi, sun dusar da tagomashin City, inda har Chelsea ta zubar da wata babbar dama wacce mai tsaron gidan City ya cafke.
Wasu na ganin fargaba ce ta mamaye ‘yan wasan Pep Guardiola da farko, saboda wannan shi ne karon farko da suka kai ga zuwa wasan karshe a wannan gasa, yayin da wannan karo shi ne na uku da Chelsea take zuwa wasan karshe.
Ta ma taba lashe kofin a shekarar 2012. City ita ta lashe kofin gasar Premier na bana.
Chelsea ta zura kwallon ne jim kadan bayan ficewar Thiago Silva da ya ji rauni.
Sauran kadan Christian Pulisic ya kara kwallo ta biyu jim kadan bayan shigarsa wasan a zagayena biyu.