Babban daraktan yada labarai na jahar Kano Halilu Ibrahim Dantiye a wata sanarwa jiya laraba ya fitar da sunayen daliban da suka rasa rayukan su a wani hatsarin mota da suka yi a ranar Talatar da ta gabata.
Dalibai takwas ne suka rasa rayukan su a wani mummunan hatsarin mota akan babbar hanyar Ibadan zuwa Legas a sakamakon fashewar tayar motar.
Mujallar Daily Post ta bayyana cewa Daraktan ya ce, "dalibai bakwai sun fito ne suka rasa rayukan su a sakamakon fashewar taya akan babbar hanyar Ibadan zuwa Legas.
"Daliban wato Ahmed Faisal, da Kamal Muhammed, da Abubakar Abdullahi dalibai ne a makarantar Kano Capital School, Umar Musa, da Sani Musa, da Ibrahim Sani da Yusuf Danladi daliban makarantar Unity College Karaye ne duk a jahar ta Kano.
"Sauran wadanda suka rayukan su a hatsarin sune Aminu Abdullahi, wanda shine direban motar da kuma Okafor, ma'aikacin kamfani FrieslandsCampina WAMCO Nigeria Plc, sauran dalibai uku dake cikin motar kuma sun sami raunika daban daban".
Lamarin ya auku ne a yayin da daliban suke hanyar ta komawa gida daga gasar makarantu ta kasa da kamfanin FrieslandCampina ya shirya a jahar Legas.