Wata kotu a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, ta yanke wa wata mata mai shekaru 46 da haihuwa hukuncin daurin wata guda a gidan kaso a sakamakon kama ta da laifin satar wayoyin hannu guda biyar.
Alkalin kotun Alhaji Abubakar Sadiq, ya ba wadda ake tuhuma da aikata laifin cajin biyan kudi Naira dubu uku, da kuma ja mata kunne akan cewa ta kaurace ma ci gaba da aikata ayyukan ashsha. An yakne wa Salamatu hukunci ne akan samun ta da aikata laifuka biyu, shiga harabar wasu ba da izini ba da kuma laifin sata.
Matar ta roki kotun ta tausaya mata inda tace wannan shine karon farko data taba daukar kayan mutane, da farko mai gabatar da kara Judith Obatomi ya bayyanawa kotun cewa wasu masu gadin wani asibiti dake Gwarimfa ne suka damke matar sa'an nan suka hanunta ta ga ofishin 'yan sanda dake gwarimfa.
Ya kara da cewa matar ta shiga cikin harabar asibitin inda take karyar rashin lafiya inda taje daya daga cikin dakin jiyyar ta sato wayar hannu guda, daga karshe ta bayyana cewa an cafke matar ne a yayin da take kokarin shiga taxi domin tserewa.