Yana da matukar muhimanci mutane, su san mai suke rubutawa a shafufukan su na zumunta, a yanar gizo, kamar su facebook, twitter, instagram, da dai makamantan su. Sau da dama mutane kan rubuta abubuwa batare da la’akari da irin abun da kanje ya dawo ba.
Jeanette Garza, ta shiga cikin tsaka mai wuya, wanda tayi rubutu a shafin ta na facebook. Hakan ya kaita ga danasani, domin kuwa an gurfanar da ita. Tana da ‘yaya uku, inda ta rubuta cewar “Da akwai wanda ‘yayan shi suke zuwa makarantar Sierra?” Hakan yasa jami’ai tunanin mai yasa ta rubuta hakan?
Ta bayyanar da cewar danta, da ke zuwa wata makarantar firamari, kimanin makonni da suka gabata ya gaya mata cewar, wasu yara a makarantar su ta firamari, suna shirin zuwa da bindiga don harbawa suga wazai fara mutuwa. Bata yi wani kokari ba wajen sanar da hukumomi ba, wanda hakan yasa aka daura laifin a kanta. Alkali ya yanke mata hukuncin kwanaki talatin a gidan kasu, da tarar dallar Amurka $29 dai-dai da naira dubu goma.