Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar "FIFA" Ta Tuna Da Rasheed Yekini!


Rasheedi Yekini
Rasheedi Yekini

A jiya ne Laraba hukumar kwallon kafar duniya “FIFA” ta tuna da shahararren dan wasan kwallon kafar nan Rasheed Yekini, wanda yake cika shekaru hudu da mutuwa. An dai bayyanar da mamacin da cewar hazikin dan wasa ne da kasar Najeriya, baza ta taba mantawa da shi ba.

A lokacin wasan shi ya saka kwallaye guda talatin da bakwai 37 a raga. Yekini, dai ya mutu ne bayan wata gajeruwar rashin lafiya, a ranar 4 ga watan Mayu na shekarar 2012, Allah yai mishi rasuwa. Ya mutu yana da shekaru arba’in da takwas a duniya (48).

Tarihin duniya ba zai taba cika ba batare da an anbato irin nasarar da ya samoma kungiyar kwallon kafar Najeriya ba, ta “Super Eagle” a wasan U.S.A 1994. Inda suka yima kasar Bulgaria ci 3 da babu. An tuna da shi da kuma fatar Allah yayi mishi rahama.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG