Kungiyoyi da jami’yun siyasa a jihar Taraba, sun bukaci Gwamnatin jihar da ta hanzarta kafa kwamitin bincike domin bankado masu hannu akan badakalar bacewar wasu kudade da kayayyakin Gwamnatin jihar ta Taraba.
Kamar yadda bayanai ke nunawa wasu jami’an Gwamnatin da ta shude sun yi awon gaba da wasu kayayyaki ana daf da mika mulki ga sabuwar Gwamnati, kayayakin da ake zargin an kwashe sun hada da wasu motoci dake gida Gwamnati da kuma wasu kayayyaki na miliyoyin Naira, a gidan tsohon mukaddashin Gwamnan jihar.
Babbar jami’yyar adawa ta APC, a jihar ta bakin shugabanta Alhaji Jika Ardo, ta nuna bacin ranta bisa abun da ta kira wakaci katashi da dukiyar jihar, shugaba yace zasu dauki matakan sharia, domin gurfanar da wadanda ake zargi a gaba kotu.
Wannan dai na zuwane yayin da ita kanta Gwamnatin jihar ke ikirarincewa ta gaji dinbin basussuka daga Gwamnatin da ta gada baya da kayayyakin da aka wawushe.