Wai ina aka kwana akan samari masu gudun ‘yanmatansu idan watan Azumi ko watan Maulidi suka tsaya? Wasu ‘yan mata da suka bayyana nasu damuwar suce, ai duk namijin dake son mace, to ba zaiji kashin yimata wannan siyayar ta wadannan lokuttan ba.
Wata da tace ita bata da bukatar a kawomata wani abu, amma dai gaskiya idan ta fahimci saurayi ya daina zuwa wajenta saboda kawai kada ya kawomata wadannan abubuwane, to gaskiya zata rabu dashi, duk dai dacewar wannan bashi ke nuna soyaya ba amma wannan na nuna wasu alamu na kadamu da mace.
Ai duk wanada yadamu da masoyiyarshi, to ba wai kayan azumi ba koda kuwa cewa akayi ya kawo garinsu baki daya, aikowa zaiyi don kauna dake tsakaninsu, amma idan ya gaza to wannan na iyanuni dacewar koda kin aureshi, bazai iya tsare miki wasu lalurorinki kenan ba. Babban abun nuni a nan shine yakamata matasa su sani, wannan kai kayan ba wai farilla bane, illa dai kyautatawa a rayuwace kawai, da kuma nuna kauna ta har’abadan. Yakamata samari masu irinwannan halin su sake dubawa.