Daruruwan daliban Jami’ar, Olabisi Onabanjo, Ago Oye, dake jihar Ogun, sun yi wata zanga zanga, na nuna takaicin su a game da mutuwa takwarorinsu goma sha biyu maza bakwai mata biyar a sakamakon wani taho mu gama da wata babbar mota akan hanyar Shagamu zuwa Lagos.
Daliban da yawancinsu ke sanye da bakaken tufafi shun cunkushe kan titin Ago Oye, suna tafiya suna rera wakokin Allah tsine ga direban da yayi sanadiyar mutuwar dalibai goma sha biyu .
Zanga zangar daliban dai ta jawo cunkoson motoci akan titi tare da gurgunta harkokin kasuwanci, da yake jawabi shugaban daliban Adelola Adegbesan, yace suna yin zanga zangar ne don su nuna bakin cikinsu a game da kashe masu dalibai da wani direba mai ganganci yayi wadanda basu bin dokokin hanya, ya kuma kalubalanci hukumar kiyaye haddura da cewa basu yi komai ba game da abun da ya faru.