A cikin watan ramadana babban abu da yakamata ace kowane mahaluki nayi shine aikin nemana kusanci da Allah, amma wasu samari kanyi amfani da lokacinsu wajen wasu ayyuka da basu da wani alfanu.
Wasu matasa da suka bayyanar da nasu irin rage lokacin, wanda sukace suna ganin dasu kasance suna tsegumin wasu ko wasu abubuwa da basu kamata ba, sai suka kirkiroma kansu da abunyi, wanda sukeyin wasan “Karta” amma wannan wasan da sukeyi basunayi shi da kudi bane, kowani abu daya haramta yinta ba. Su dai suna wannan wasanne don nishadi da kuma kokarin fahimtar junansu.
Babban dalilin da yasa suke wannan wasan shine ganin yadda basu da abunyi, basu da wata sana’a, sai sukaga da su sa kansu cikin wasu abubuwan ki, gara su samar da abunda zai kautar dasu daga munanan, tunani da kan iya sasu cikin hallaka. Suna kuma fatar Allah, yasa shuwagabannin su sama masu ayyukanyi batare da sun zauna bawani abu da zasu taimakam cigaban kasarsu baki daya ba.