Sudan: ‘Yan Najeriya 131 Sun Sauka A Abuja

'Yan Najeriya da aka kwaso daga Sudan (Hoto: Twitter/NIDCOM)

A ranar Juma’a wani rukuni na biyu dauke da mutum 130 ya sauka a birnin Abuja daga Port Sudan.

Rukuni na uku na tawagar ‘yan Najeriya da ke tserewa rikicin Sudan ya sauka a Abuja, babban birnin kasar a ranar Asabar.

“Manya 124 da jarirai bakwai da suka taso daga Port Sudan, sun sauka a filin tashin jirage na Nnamdi Azikwe da ke Abuja da misalin karfe 1:45 na yamma.” Hukumar da ke kula da ‘yan Najeriya da ke zaune a kasashen ketare ta NIDCOM ta a shafinta na Twitter a ranar Asabar.

A ranar Juma’a wani rukuni na biyu dauke da mutum 130 ya sauka a birnin Abuja daga Port Sudan.

Tun a makon da ya gabata Najeriyar ta bi sahun sauren kasashen duniya wajen kwashe ‘yan kasarta a kasar wacce ke fama da rikici.

Fada ya barke ne a ranar 15 ga watan Afrilu tsakanin dakarun kasar da na sojojin RSF na musamman, inda kowannen su ke kokarin karbe ikon kasar.

Akalla mutum sama da 400 sun mutu yayin da dubbai suka jikkata a rikicin.