A watan Oktoban bara ne Sudan da Iran suka amince su maido da huldar diflomasiyya, yayin da gwamnatin da ke goyon bayan sojojin kasar ke fafutukar neman abokan hulda a lokacin yakin da ta ke yi da dakarun RSF.
Gwamnatin Sudan, wadda ke mara wa sojojin kasar a yakin da suka shafe watanni 15 suna yi da dakarun RSF, a cikin wata sanarwa ta fadi cewa Burhan ya karbi bakuncin sabon jakadan Tehran Hassan Shah Hosseini a birnin Port Sudan.
Birnin Port Sudan da ke gabar tukun bahar maliya ya zama shelkwatar gwamnatin Sudan yanzu, tun bayan da yaki ya daidaita birnin Khartoum.
Wannan shi ne "mafarin wani sabon babi na dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu," a cewar karamin sakataren ma'aikatar harkokin wajen kasar Hussein al-Amin yayin da Burhan ya tura Abdelaziz Hassan Saleh zuwa Iran a matsayin sabon jakadan Sudan.
A shekarar 2016 ne Sudan ta daina hulda da Iran a wani mataki na nuna goyon bayanta ga kasar Saudiyya, bayan da aka kai wa ofishin jakadancin Saudiyya hari a Tehran sakamakon hukuncin kisa da Saudiyyar ta aiwatar kan wani fitaccen malamin Shi'a.
Kasashe abokan huldar Saudiyya a yankin da yawa su ma sun yanke hulda da Iran a lokacin.
Ko da yake, a watan Maris na shekarar 2023, Riyadh da Tehran suka sanar da farfado da dangantaka tsakaninsu bayan wata yarjejeniya da China ta taimaka aka kulla.
Tun daga lokacin Iran ta dauki matakin kulla ko farfado da dangantakarta da kasashen Larabawa makwabtan ta.
Tun lokacin da aka fara yakin Sudan a watan Afrilun shekarar 2023, kasashe da yawa sun goyi bayan dakarun da ke adawa da gwamnatin.
A watan Disamba, Sudan ta kori jami'an diflomasiyya daga Hadaddiyar Daular Larabawa, bisa zargin cewa kasar da ke yankin Gulf na tura wa rundunar RSF makamai, zargin da Hadaddiyar Daular Larabawa ta musanta.
A watan Fabrairun da ya gabata, Amurka ta bayyana damuwa game da wasu makamai da Iran, kasar da basa ga majici da Washington ta tura wa sojojin Sudan.
A daidai wannan lokacin, sojojin suka kwato wasu yankuna bayan an kwashe watanni dakarun RSF na samun galaba akansu.
Hakazalika, a baya-bayan nan Sudan ta kara kusantar Rasha.