Sudan Da Hadaddiyar Daular Larabawa Sun Sami Rashin Jituwa

Taron kasashen larabawa

Wakilan Sudan sun zargi Hadaddiyar daular larabawa da taimaka wa dakarun RSF ta hannun mayakan sa-kai dake Chadi, kudancin Libya da kuma birnin Khartoum.

Wakilan Sudan da na Hadaddiyar Daular Larabawa wato UAE sun sami rashin jituwa a jiya Talata a Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, game da zargin da Sudan ta yi na cewa Abu Dhabi na bayar da makamai da tallafi ga dakarun rundunar kar ta kwana na Sudan (RSF), lamarin da ke ruruta wutar mummunan yakin Sudan.

"Ya zama wajibi UAE ta nisanci Sudan!" abinda Jakadan Sudan Al-Harith Idriss Al-Harith Mohamed ya shaida wa kwamitin sulhun na Majalisar Dinkin Duniya ke nan. Ya kara da cewa, "Wannan ita ce bukata ta farko da zata bada damar samar da zaman lafiya a Sudan."

Mohamed ya zargi Hadaddiyar daular Larabawan da taimaka wa dakarun RSF ta hannun mayakan sa-kai dake Chadi, kudancin Libya da kuma birnin Khartoum, don tabbatar da ikirarin katsalandan din da UAE ke yi. Ba tare da bayar da shaida ba ya kuma fadi cewa, ana kwashe mayakan rundunar RSF da suka jikkata zuwa Dubai ta jirgin sama don a yi musu jinya a can.