A yau Juma’a ne dubban mutane Barcelona sukayi shiru na tsawon minti guda domin girmamawa da tunawa da wadanda harin da aka kai da mota jiya ya rutsa da su, wanda mutane 14 suka rasa rayukansu wasu sama da 100 suka jikkata.
Sarkin Spain kuma Farai Minista, Mariano Rajoy ya halarci taron jimamin da aka gudanar a dandalin Placa de Catalunya. Fara Ministan Spain ya ayyana kwanaki uku domin zaman makoki a kasar.
Wannan lamari dai ya faru ne a jiya Alhamis lokacin da wani dan ta'adda ya sheko da mota kan wasu jama'a da ke tafiya, ya hallaka mutane 13 ya kuma raunata sama da 100.
Matukin babbar motar da ya kai harin ya arce da ‘kafa wanda har yanzu ake nemansa. ‘Yan Sanda sun kama mutane biyu a jiya Alhamis, amma ya zuwa yanzu babu wani bayani dake nuna yadda mutanen biyu ke da alaka da harin. An kuma kama mutum na uku a yau Juma’a a Arewacin Catalan na garin Ripoll, a cewar Ministan cikin gida Joaquim Form.
A wani hari makamancin wannan ‘yan Sa’o’i a garin Cambrils, wata mota ta afkawa wasu masu tafiya a kafa da wata motar ‘yan Sanda. ‘yan sandan dai sun kashe maharin, wanda suka ce yana dauke da abin fashewa a jikinsa.