Son Zuciya Da Kwamacalar Siyasa Suka Haddasa Rikicin Rivers

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya yana jawabi a Port Harcourt

Dr. Usman Mohammed yace neman kujerar siyasa a zaben 2015 daga fadar shugaban kasa, shi ne ummul haba'isin rikicin da ake yi a majalisar Rivers
Mai fashin baki Dr. Usman Mohammed, yace son rai da kuma neman mukaman siyasa, sune suka rufewa shugabanni idanu har ta kai ga dambarawar siyasar da ake yi yanzu haka a Jihar Rivers.

Dr. Mohammed, yace wannan kwamacalar siyasa, ta samo asali ne tun daga fadar shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, inda siyasar "ayi yadda nace, ko a bata baki daya" ta zamo taken yadda al'amura suke gudana.

A cikin hirar da yayi da Sashen Hausa na Muryar Amurka, masanin siyasar yace wannan abu ya fito fili a wasu abubuwan dake faruwa, inda fadar shugaban kasa ta bayyana goyon bayanta ga bangaren marasa rinjaye na Kungiyar Gwamnonin Najeriya, domin wanda yaci zaben a zahiri, watau gwamna Rotimi Amaechi, ba dan lelen shugaban kasa ba ne.

Yace bai ga yadda za a ce 'yan majalisa kwaya biyar tak, wadanda ke samun daurin gindin fadar shugaban kasa, zasu iya fin karfin sauran 'yan majalisa su 27, har ma a ce an kai ga fitinar da zata sa majalisar wakilai ta kasa ta kwace ayyukan majalisar dokokin Jihar.

Malamin, yace idan ba a maida hankali ba, wannan mataki ne da zai iya yin illa sosai ga tafarkin dimokuradiyya a kasa.

Ga bayanin malamin nan...

Your browser doesn’t support HTML5

Son Zuciya Da Kwamacalar Siyasa Suka Haddasa Abinda Ya Faru A Jihar Rivers - 1:52