Hukumomin a yankin Puntland na kasar Somalia mai cin kwarya-kwaryan gashin kansa, sun ce sun kama wani jirgin ruwa makare da makamai, kamar yadda suka bayyanawa Muryar Amurka.
Mukaddashin ‘yan sandan yankin, Mohammed Mohamud Hassan ya ce, makaman sun hada da manyan bindigogi nau’in AK47 da bindigar kakkabo jiragen sama da kuma harsashai.
A cewar shi, sun kama jirgin ne yayin da yake kokarin tserewa a kusa da yankin gabar ruwan Mareero da ke da tazarar kilomita tara daga gabashin yankin Bosaso, yanki mafi girma da ke dauke da tashar jiragen ruwa da kuma yawan hadahadar kasuwanci.
Yayin da suka baje makaman a gaban manema labarai, hukumomin kasar sun ce suna gudanar da bincike domin gano ko na wane ne makaman, sannan kuma ina aka dosa da su.