Samar da cigaba mai dorewa domin inganta rayuwar al'ummomin yankin Afirka ta Yamma dai dai da kudurin Majalisar Dinkin Duniya, MDD, shine jigon maudu'in da masana zasu baje a yayin wannan taro na shekara shekara na kungiyar jami'o'in Afirka ta Yamma da yanzu yake gudana a Yamai.
Shugaban Jami'ar Ilorin Farfasa Abdulganiyu Ambali bugu da kari shugaban kungiyar jami'o'in kasashen yammacin Afirka ya yi karin bayani akan manufar taronsu. Yana mai cewa babu yadda mutum zai yi rayuwa idan babu kwanciyar hankali. Saboda haka jami'o'i na bincike akan rayuwar mutum da zaman lafiya. Babu abun da za'a iya yi idan babu zaman lafiya. Cigaba ya ta'allaka ne akan zaman lafiya.
Wannan taron shi ne karo na biyar da jami'o'in kasashen yammacin Afirka zasu yi tare tun lokacin da aka kafa kungiyar a shekarar 2011.
Shugaban Jami'ar Abdulmummuni ta Yamai Farfasa Habibu Abarshi yana kallon taron nasu a matsayin na karawa juna sani ne. Yana mai cewa idan sun hadu suna iya taimakawa juna da abun da kowa ya kware a kai. Yin hakan shi ne zai kawo bunkasa. Taron shi ne ya kawo hadin kai ta yadda zasu taimakawa juna.
Bullo da shawarwari masu alfanu da shirin ciyar da kasashen Afirka ta Yamma gaba shi ne abun da mahukumta ke fatan samu daga taron, inji ministan ilimi mai zurfi na jamhuriyar Nijar Yahuza Salisu. Yana mai cewa gwamnatin Nijar na jiran su gabatar mata da abubuwan da suka tattauna da shawarwarin da suka bayar wadanda a tunanensu idan gwamnatoci suka bisu zasu cimma buri. Idan sun bayar, su, a gwamnati zasu yi nazari a kai.
Karancin kudaden gudanarwa na cikin kalubalen da jami'o'in ke fuskanta dalili ke nan da zasu tantance wannan maganar a taronsu su kuma gabatar wa gwamnatocin kasashensu bayan sun kammala taron gobe.
Ga rahoton Souley Mummuni Barma da karin bayani.
.
Facebook Forum