Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Adawan Siyasa a Nijar Sun Yi Watsi da Tayin Taron Sasantawa


Firayim Ministan Nijar Birji Rafini
Firayim Ministan Nijar Birji Rafini

Firayim Ministan Nijar shi ya kira taron sasanta alamuran zabuka dake zuwa tare da 'yan adawa domin kaucewa wasu matsaloli

Firayim Ministan kasar Nijar Birji Rafini ne ya kira taron tattaunawa a jiya Lahadi tsakanin masu rinjaye da 'yan adawa domin samun masalahar da zata kawo karshen kallon hadarin kajin da bangarorin biyu ke yiwa juna.

Taron na cikin wani shirin share fagen kafa sabuwar hukumar zabe ne, sai dai ana gap da taron jam'iyyun adawa suka yi watsi da tayin bisa ga wasu dalilan da suka bayyana a wata wasika da suka aikawa gwamnati.

Ministan cikin gida shi ya yi bayani, yana mai cewa su 'yan adawa na ganin babu dimokradiya a kasar yanzu. Suna bukatar a shirya taron kasa gaba daya tare da wakilan kasashen waje da zasu zama shaidu domin a mayar da Nijar bisa tafarkin dimokradiya.

Shugaban jam'iyyar ORDN ta 'yan adawa Mamman Sani Adamu yana mai cewa wanda bai yadda da sabanin ra'ayi ba da adawa, da 'yan adawa su fadi albarkacin bakinsu a kafofin yada labarai ba zai yi zancen zabe ba. Duk wanda bai mutunta dimokradiya ba wane zabe kuma yake so, inji Adamu.

Rashin halartar taron da 'yan adawa suka yi ya sosawa masu rinjaye rai dake cewa zasu dinga bin 'yan adawa da laluma.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG