Kakakin gwamnantin kasar Kamaru Isa Ciroma Bakari shi ya bayyanawa manema labarai batun fashewar bamabamai a garin Bamenda fadar gwamnatin jihar arewa maso yammacin Kamaru da take anfani da harshen ingilishi wadda kuma ta dade tana adawa tare da nuna kin jinin gwamnatin Paul Biya.
Yayinda yake jawabi a birnin Yaounde fadar gwamnatin kasar Kamaru Bakari yana mai cewa "ba zamu taba yadda da irin wadannan 'yan ta'adda su dinga zuwa cikin kasarmu suna bata mana kasarmu ba...Dole ne mu jajirce wajen ganin cewa mun dakile irin wannan ta'addanci a kasarmu".
Harin na Bamenda ya jikata dakarun tsaro uku da aka garzaya dasu asibiti.
Gwamnan jihar Bamendan Adock Afrique shi ma ya nuna bakin cikinsa da aukuwar lamarin. Ya kira jama'ar jihar da su bi doka da oda kuma su lura kada su bata zamantakewar dake tsakaninsu da suka gadadaga iyaye da kakanni.
Gwamnan ya kara da bada tabbacin zasu gudanar da bincike kan lamarin domin zakulo bata garin.
Ga rahoton Awal Garba da karin bayani.
Facebook Forum