Sokoto: 'Yan Bindiga Sun Sace Sarkin Gobir

Sarkin Gobir na Gatawa Isah Muhammad Bawa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, ASP Ahmad Rufa’i, ya tabbatar wa da Muryar Amurka cewa, ‘yan bindiga sun sace Sarkin Gobir tare da dan sa.

Matsalar rashin tsaro na ci gaba da hana mutane bacci da idanu biyu rufe a wasu sassan Najeriya duk da kokarin da mahukunta ke yi na samun saukin matsalar.

Wani abu da ke kara tabbatar da haka shi ne yadda 'yan bindiga a ranar Asabar su ka sace basaraken daular Gobir da ke Sokoto, Sarkin Gobir na Gatawa Isah Muhammad Bawa.

Yanzu haka 'yan uwa da sauran jama'ar gari na ci gaba da nuna alhini a kan wannan lamari da ya faru da Sarkin Gobir wanda ba da jimawa ba ne aka sauya masa wurin aiki zuwa Gatawa, irin abin da ya jima yana addabar jama'ar yankin na gabashin Sokoto, duk da yake sun jima suna kokawa a kan su samu saukin matsalar.

Sirajo Isah, Da ne ga Sarkin Gobir kuma ya bayyana yadda lamarin ya faru, ya ce Sarkin yana dawowa ne daga Sokoto, ya kawo wurin da ake kira kwanar maharba, cikin Sabon Birni nan ne barayin su ka tare motar sa suka ja shi tare da direba bayan sun yi wa motar harbi biyu.

Ya ce jami'an 'yan sandan Mopol da su ka zo kawo dauki suma barayin sun tarbe su cikin duhun shukar su ka yi ta musayar wuta tsakanin su, amma karshe dai barayin sun tafi da Sarki da kuma dan sa wanda shi ne ke jan motar da su ke ciki.

Duk da yake ya yaba akan kokarin da jami'an Mopol su ka yi, ya ce mahukunta da su yi mai yuwa wajen ganin an ceto Sarkin da dan sa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, ASP Ahmad Rufa’i, ya tabbatar wa Muryar Amurka cewa ‘yan bindiga sun sace Sarkin Gobir tare da dan sa.

Jim kadan bayan sace Sarkin wasu rahotanni sun nuna cewa, an sake sace wasu mutane biyar duk a garin na Sabon birni, a kan haka ne ma jama'ar garin ke kara yin kira ga mahukunta.

Har yanzu a Gabashin Sokoto a iya cewa 'yan bindiga na cin karen su ba babbaka, domin duk matakan da mahukunta ke cewa suna dauka sun kasa kare da jama'a daga ayyukan barayin.

Wani abu da jama'a su ka yi fatar ya kawo musu sauki, shi ne matasan nan da gwamnati ta bai wa horo, don su taimaka wajen samar da zaman lafiya da aka yaye tun ranar 9 ga watan Maris na wannan shekara, sai dai kawo yanzu duk da kayan aiki da aka nunawa jama'a cewa za'a basu ba a basu ba.

Tunanin faruwar hakan ne ya sa wasu jagorori na yankunan da ke fama da tsaro suka nuna shakku tun daga farko, kamar yadda dan majalisar Isa ya nuna a wata ganawa da nayi da shi lokacin yaye matasan.

Duk kokarin da Muryar Amurka ta yi na jin ta bakin gwamnati a kan yaushe za'a bai wa wadannan matasa kayan aiki ko za su iya taimakawa ga samun saukin matsalar, sai dai babu amsa, domin duk jami'in da aka kira baya iya magana.

Wannan matsalar ta rashin tsaro kusan a iya cewa tana ci gaba da zama kulli gagara kwanta a wasu jihohin Najeriya.

Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:

Your browser doesn’t support HTML5

Sokoto: 'Yan Bindiga Sun Sace Sarkin Gobir 3'32".mp3