Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: ‘Yan Bindiga Sun Sace Wasu Matafiya A Hanyar Shagamu


Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun (Facebook/Rundunar 'Yan sandan Najeriya)
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun (Facebook/Rundunar 'Yan sandan Najeriya)

Jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola, ta tabbatar da sace wani direba da wasu mutane dauke da makamai suka yi a hanyar Ijebuode/Sagamu.

Kimanin matafiya 20 ne rahotanni suka ce wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da su a hanyar Sagamu-Ijebu-Ode a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Rahotanni sun ce an yi wa matafiya kwanton bauna ne a ranar Lahadin da ta gabata, a kewayen yankin Sagamu kusa da rundunar ‘yan sandan Najeriya da kuma garin Ilishan.

Wani mazauni kuma shugaban hukumar yankin Ilishan, Wemmy Osude, ya shaidawa gidan talabijin na Channels cewa an harbi wani mutum a gwiwa a lokacin da lamarin ya faru.

Ya tabbatar da cewa daya daga cikin wadanda harin ya rutsa da su, mazaunin Ilisan Remo, yana karbar kulawa a asibitin koyarwa na jami’ar Babcock bayan da ‘yan bindigar da ake zargi suka harbe shi a gwiwarsa.

Osude ya kara da cewa ya yi magana da mazaunin garin da ke karbar magani. "Yana cikin kwanciyar hankali," in ji shi.

Ya kuma bayyana tattaunawa da kwamandan yankin Sagamu da lamarin ya faru, inda ya bayyana fatan jami’an tsaro za su bi sahun masu laifin tare da kubutar da mutanen da aka sace.

Jami'ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola, ta tabbatar da sace wani direba da wasu mutane dauke da makamai suka yi a hanyar Ijebuode/Sagamu.

Ta kuma bayyana cewa, an yi fashi da makami sau uku a wuri guda.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG