Wasu hare-hare da ‘yan bindiga suka kai a kauyukan Tureta dake jihar Sakkwato sun yi sanadin salwantar rayuka fiye da ashirin.
Hare-haren ‘yan bindiga na ci gaba da hana jama'a bacci da ido biyu rufe a sassa daban daban na arewacin Najeriya domin koda yaushe jama'a na cikin fargabar yuwuwar fuskantar harin ta'addanci .
A jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya ‘yan bindigar na ci gaba da matsa lamba wajen kai hare-hare suna kisa da satar dabbobi da dukiyoyin jama'a, kamar hare-haren da suka kai a garurawan da ke karamar hukumar Tureta wadda ke makwabtaka da jihar Zamfara.
Shugaban karamar Abubakar Salihu Tureta yace kwananan barayin sun matsawa jama'a.
Wani hari da suka kai garin tsamiya shi ne yayi sanadin salwantar rayukan jama'a wadanda suka fada ruwa wurin gudun tsira daga maharan.
Wani mazaunin Garin na Tureta Umaru S Makafi Tureta da Muryar Amurka ta zanta da shi, yace hakika kauyukan Tureta na fuskantar matsalolin rashin tsaro.
Duk da yake shugaban karamar hukumar yace rundunar ‘yan sanda da sauran jami'an tsaro na da masaniya akan wadannan matsalolin, na yi kokarin kiran kakakin rundunar ‘yan sanda a Sakkwato DSP Sanusi Abubakar, domin jin ta bakin su, amma yaki daukar dukan kiran da nayi masa.
Masana dai na ci gaba da bayar da shawarwari akan yadda watakila za'a iya samun saukin matsalolin rashin tsaron, kamar yadda Dokta Yahuza Ahmad Getso ke fada.
Yanzu dai da yawa ‘yan Najeriya da ke ganin gazawar gwamnati ga shawo Kan matsalolin rashin tsaro musamman duba da yadda ‘yan bindiga ke nuna gabara ga hare-haren da suka kaiwa.
Saurari cikakken rahoton cikina sauti:
Your browser doesn’t support HTML5