Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan bindiga Sun Sace Mutane Sama Da 10 A Yankin Wurno Na Jihar Sakkwato Ta Najeriya.


A Najeriya al'ummomi na kara shiga damuwa sanadiyyar ayyukan ‘yan bindiga wadanda ke hana su bacci da ido biyu rufe, abin da wasu jagororin al'umma ke ganin ya dace mutane su tashi su kare kansu.

SOKOTO, NIGERIA - A wannan makon ‘yan bindiga sun kai hari a yankin Wurno na jihar Sakkwato a arewa maso yammacin Najeriya inda suka yi garkuwa da mutane goma sha daya.

Har yanzu dai tsugune bata kare ba ga ‘yan Najeriya domin duk da matsalolin rayuwa da talaka ya tsinci kansa ciki, zaman lafiya ma ya gagara musamman a yankunan talakawan da ke arewacin kasar inda ‘yan bindiga ke cin karensu ba babbaka.

Yankin gabashin Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya, a iya cewa, babu inda jama'a ke da cikakken kwanciyar hankali a dukan kananan hukumomi takwas da ke yankin.

Yankin Wurno da ke gabashin na Sakkwato kwananan ya sake daukar bakuncin mahara, kamar yadda jagoran al'ummar yankin ya tabbatar mana.

Shi kuwa basaraken garin Dinawa, inda aka sace mutane shida, ya ce wannan ba shi ne karon farko ba da ‘yan bindiga ke hana wa jama'a kwanciyar hankali.

Yankin Sabon birni ma duk da kokawar da jama'ar yankin ke yi a kan matsalolin rashin tsaro, lamarin na ci gaba da wanzuwa, kamar yadda wani mazaunin garin Tarah ya shaida mana.

Mun nemi jin ta bakin jami'an tsaro sai dai abin ya ci tura, domin kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Sakkwato, DSP Sanusi Abubakar, bai dauki kiran da muka yi masa ba.

Duba da yadda matsalolin rashin tsaro suka gagari gwamnatin Najeriya ne, ya sa masana harkokin tsaro ke bai wa jama'a shawarwari ko da za su samu saukin matsalolin idan suka gwada amfani da su.

Bisa ga yadda lamuran rashin tsaro ke tafiya a Najeriya, ‘yan kasar na ci gaba cire kauna ga iyawar mahukunta wajen magance wannan matsalar, wadda ke ci gaba da wanzuwa duk da kokarin da hukumomin ke yi.

Saurari rahoton daga Muhammadu Nasir:

‘Yan bindiga Sun Kai Hari A Yankin Wurno Na Jihar Sakkwato Inda Suka Yi Garkuwa Da Mutane Goma Sha Daya.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

XS
SM
MD
LG