Abinda ke nuna hakan shine yadda ‘yan bindigar suka sace mutane tamanin da daya rana daya a karamar hukuma daya a jihar Sakkwato.
Lamarin ‘yan bindiga na ci gaba da ta'azzara tare da kure tunanin ‘yan Najeriya musamman na arewacin kasar.
A jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin kasar ‘yan bindiga yiwa karamar hukumar Sabon Birni kawanya ranar litinin ta wannan mako suka sace mutane a kauyuka daban daban tare da kashe mutum biyu.
Honarabul Aminu Almustapha Boza Dan majalisar jiha mai Wakiltar jama'ar karamar hukumar ya bayyana yadda hare haren suka faru inda ya ce 'yan ta'addan, da ma sun zagaye manoma, shi ya sa suka dinga bin kauyuka-kauyaka suka dinga sace mutane tare da kashe wasu.
Wannan na zuwa ne lokacin da rundunar 'yan sanda ta fitar da wani bayani cewa ta kama ‘yan sa kai 6 akan tuhumar kisa, sata da kona gawar wani dattijo dan shekara 90 a garin Gwadabawa a jihar ta Sakkwato.
Sai dai Muryar Amurka ta nemi ta ji ta bakin kakakin rundunar, DSP Sanusi Abubakar akan hare haren da aka kai a Sabon Birni, amma rashin kyawon sadarwa daga wuri sa ya hana magana.
Matsalolin rashin tsaro a Najeriya dai da yawa jama'a ke ganin ya gagari mahukunta abinda ya sa wasu jama'a suka dukufa ga neman daukin Ubangiji ga maganin matsalolin.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: