SOKOTO: Hadarin Kwalekwale Ya Salwanta Rayukan Jama'a

Ana Ci Gaba Da Gano Gawarwakin Wadanda Suka Raso A Hatsarin Jirgin Ruwa A Sakkwato

A Najeriya har yanzu ana samun salwantar rayukan jama'a sanadiyar hadarin kwalekwale duk da matakan da mahukunta ke cewa suna dauka na magance irin wannan matsalar.

Wannan na zuwa ne lokacin da aka kara samun hadarin kwalekwale da sanyin safiyar yau Talata a kauyen Dandeji da ke karamar hukumar Shagari a jihar Sakkwato wanda ya yi sanadin salwantar rayukan da basu kasa 15 ba, akasari yara kanana.

Wannan hadarin ya kasance daya daga jerin hadurran kwalekwale da ke zama sanadin salwantar rayukan ‘yan Najeriya musamman mazauna yankunan da ke da ruwa.

Wani mutumin yankin da lamarin ya faru a gundumar Lambara ta karamar hukumar shagari Muhammad Jabbi Ibrahim yace yara ne ‘yan mata da yawan su ya kai kimanin 40 suke zuwa neman itace dafa abinci suna tsallaka ruwa lokacin da abin ya faru.

Yace an samu lalabo gawar yara 15 daga cikin su, amma dai ana ci gaba da aikin ceto.

Kantoman karamar hukumar Aliyu Dantanin Shagari ya tabbatar da aukuwar lamarin.

To sai dai duba da yadda hadarin kwalekwale ke ta aukuwa a yankin shagari ya sa gwamnati ta sha alwashin daukar matakai na kare aukuwar hakan. To sai dai mazauna yankin sun ce ba su gani a kasa ba.

Kantoman karamar hukumar ya ce an samar da rigunan hana nutsewa cikin ruwa da kuma kwalekwale na zamani duk da yake sun yi karanci ga bukatun yankunan.

Masu lura da lamurran yau da kullum na ganin cewa dole ne mahukunta su yi da gaske, su kuwa jama'a su kasance masu bin doka kafin a iya magance wannan matsalar.

Hadarin dai ya yi sanadin salwantar rayukan mutane da dama a Najeriya. Ko a makon da ya gabata an sami nutsewar kwalekwale a jihar Zamfara wanda ya hallaka rayuka da dama.

Ayankin na shagari ma an sami salwantar daruruwan rayuka sanadiyar hadarin kwalekwale.

Saurari rahoton a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

SOKOTO: Hadarin Kwalekwale Ya Salwanta Rayukan Jama'a