Sojojin Sudan Da Dakarun RSF Sun Yi Arangama A Khartoum

An gwabza fada tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF A Khartoum da wasu wurare a kasar

Kazamin fada ya barke tsakanin sojojin Sudan da babbar rundunar mayakan kasar ta RSF a birnin Khartoum da wasu wurare a kasar, lamarin da ke kara kawo fargabar ganin bazuwar tashin hankali a kasar da ke fama da rikice-rikice.

Babbar kungiyar mayakan Sudan ta ce ta kwace fadar shugaban kasa, da gidan babban hafsan sojojin kasar, da kuma tashar jiragen sama ta kasa-da-kasa dake birnin Khartoum ranar Asabar, a wani lamari mai kama da yunkurin juyin mulki, ko da yake rundunar sojan kasar ta ce tana maida martani.

Kungiyar mayakan RSF, wacce ta zargi sojojin kasar da fara kai mata hari, ta kuma ce ta kwace filayen sauka da tashin jiragen sama da ke arewacin garin Merowe da kuma El-Obeid a yammacin kasar.

Dakarun rundunar RSF na Sudan

Takamaimai dai ba a san halin da ake ciki ba. Rundunar sojan kasar ta ce tana fafatawa da dakarun RSF a wuraren da mayakan suka ce sun kwace. Haka kuma sojojin sun ce sun kwace wasu sansanonin dakarun sun kuma musanta ikirarin da suka yi na cewa sun kwace filin jirgin saman Merowe.

Sudan

Babban fada tsakanin mayakan RSF da sojojin kasar na iya jefa Sudan cikin rikici da zai bazu ko’ina, yayin da kasar ke fama da koma bayan tattalin arziki da rikicin kabilanci, sannan kuma hakan na iya kawo cikas ga kokarin da ake na yin zabe a kasar.