A wata sanarwa da kakakin hedikwatar rundunar sojojin saman Najeriya ya fitar, ta ce sojojin ‘kasa ne suka fatattaki mayakan daga yankin Bama, inda nan take jiragen yakin sama suka bi su a baya har suka iske su a wajen kauyen Bulagalaye.
Lokacin da mayakan Boko Haram suka hangi sojojin na bin su, nan take jiragen yakin sojojin suka bude musu wuta su kayi kaca-kaca da su.
A cewar wani tsohon babban hafsa a rundunar sojan saman Najeriya, Kwamanda Baba Gamawa mai ritaya, da irin wannan ci gaba ne za a iya kawar da ‘yan Boko Haram sannu a hankali. Wanda kuma ya jaddada muhimmancin amfani da karfin sojojin sama wajen cimma nasara ga abokan gaba.
Rundunar sojan saman Najeriya ta ce za ta ci gaba da kai irin wannan farmaki har sai ta ga bayan mayakan Boko Haram.
A nashi tsokacin masanin tsaro mallam Kabiru Adamu, ya nanata cewa hare-haren da rundunar sojojin sama ke kaiwa yana da matukar amfani. Sai dai inda matsalar ta ke idan mahara suka kai hari ba a samun agaji daga sojojin sama akan lokaci.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5