Sojojin Saman Najeriya Sun Hallaka 'Yan Bindga a Jihar Zamfara

Jiragen Yakin sojojin saman Najeriya samfurin Alpha Jet

Rundunar sojojin saman Najeriya dake aiki a rundunar yaki da yan bindiga a jihar Zamfara, da ake kira Operation Hadarin Daji yanzu haka na can tana luguden wuta a sansanonin yan bindiga a jihar Zamfara.

Biyo bayan samun muhimman bayanan sirri kan inda dandazon yan bindiga suka hadu a wuri guda a dajin dake karamar hukumar Birnin magaji ta jihar Zamfara, jiragen yakin sojojin saman sun kai masu wani farmaki inda kuma aka yi nasarar hallaka gomman yan ta'addan.

Farmakin ya yi sanadiyyar kashe wasu manyan kwamandojin yan bindigar a ya yin kuma da suke jana'iza, haka kuma sojojin saman sun kara afkawa 'yan bindigar inda aka kara kashe karin wasu gomman yan bindigar.

Bayanai dai sun tabbatar da jiragen yakin Najeriyar sun kashe wasu manyan yan bindigar da ba a bayyana sunansu ba kawo yanzu. Kodayake wata majiya ta tabbatarwa wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka, cewa wani jami'i a hedkwatar tsaron kasar ya tabbatar da wannan labari yana mai cewa nan gaba kadan za suyi taron manema labarai akan batun.