Sojojin Najeriya Sun Yi Hatsarin Mota A Maiduguri

Rundunar sojojin Najeriya ta "Operation Hadin Kai" a bakin aiki (Facebook/Nigerian Army).

Lamarin ya auku ne a kusa da garin Kuturu da ke kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri a jihar Borno.

Sojojin Najeriya tara sun ji raunuka daban-daban bayan da daya daga cikin motocin da suke ciki ta yi hatsari a garin Maiduguri da ke jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.

Wata sanarwa da Darektan yada labaran rundunar sojin kasar Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu ya fitar a ranar Juma’a ta ce, sojojin suna kan hanyarsu ta kai daukin gaggawa ne a wani yankin garin na Maiduguri a lokacin da hatsarin ya auku.

“Tsantsi ne ya kwashe daya daga cikin motocin sojojin wacce ke dauke da bindiga, hakan ya sa ta zame ta afka gefen hanya, lamarin da ya sa motar ta yi juyin kuli-kulin-kubura.” In ji Nwachukwu.

Karin bayani akan: Laftanar-Janar Faruk Yahaya, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu, jihar Borno, Maiduguri, Sojojin, ISWAP, Nigeria, da Najeriya.

Lamarin ya auku ne a kusa da garin Kuturu da ke kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.

“An kai sojojin tara da suka ji rauni wani asibitin soji ana ba su kulawa, amma ba a samu asarar rai ba.”

Babban hafsan sojin kasa Laftanar-Janar Faruk Yahaya ya mika jajensa ga sojojin a cewar sanarwar.

Janar Yahaya ya yaba da irin kokarin da dakarun suke nunawa wajen kai dauki, yana mai kira a gare su da su zama masu kiyayewa a duk lokacin da za su kai daukin gaggawa.

Dubban dakarun Najeriya na jibge a jihar ta Borno, inda suke yaki da mayakan Boko Haram da ISWAP.