Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Mu Ce Za Mu Tura Masu Yi wa Kasa Hidima Fagen Yaki Ba - NYSC


Shugaban NYSC, Birgediya Janar Shu'aibu Ibrahim (Twitter/@officialnyscng)
Shugaban NYSC, Birgediya Janar Shu'aibu Ibrahim (Twitter/@officialnyscng)

“Muna so mu fayyace cewa, an yi wa bayanin Darekto-Janar na NYSC mummunar fahimta, wacce ake ta yadawa a shafukan sada zumunta.”

Hukumar NYSC mai kula da sha’anin masu yi wa kasa hidima a Najeriya, ta ce ba ta da niyyar tura wani mambanta fagen yaki.

Rahotanni dama a ranar Laraba sun ruwaito shugaban hukumar Birgediya Janar Shu’aibu Ibrahim yana cewa za a iya tura masu hidima zuwa fagen yaki kamar yadda ya bayyana wani shirin gidan talabjin na Channels.

“Babu wani lokaci da Janar Ibrahim ya bayyana cewa za a tura masu yi wa hidima zuwa fagen yaki.” Wata sanarwa da NYSC ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce.

“Muna so mu fayyace cewa, an yi wa bayanin Darekto-Janar na NYSC mummunar fahimta, wacce ake ta yadawa a shafukan sada zumunta.”

“Abin da Darekto Janar ya ce shi ne, kamar yadda tsarin tsaron kasa ya tanada, masu yi wa kasa hidima, kamar sojoji ne da aka ajiye a matakin shirin ko-ta-kwana, saboda suna da ilimi da kwarewar da za a iya horar da su a matsayin sojoji.” Sanarwar ta kara da cewa.

Hakan na faruwa ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan a soke shirin na yi wa kasa hidima, wanda ya zama wajibi ga duk wanda ya kammala karatun jami’a ko na babbar kwalejin kimiyya ta polytechnic, muddin bai kai shekara 30 ba.

A kwanakin da suka gabata ne majalisar wakilan Najeriya, ta fara muhawara kan kudurin dokar yiwuwar soke shirin, wanda gwamnatin mulkin soji ta Janar Yakubu Gowon ta kirkira a shekarar 1973, a wani mataki na hada kan kasar bayan yakin basasa da Najeriyar ta fuskanta.

Akan tura mambobin na NYSC zuwa sassan kasar har tsawon shekara guda, kafin daga bisani a sallame su, su shiga neman aiki.

Tuni har kudurin dokar neman soke shirin ya kai matakin karatu na biyu a majalisar ta wakilai, amma wasu dama a Najeriyar sun nuna rashin dacewar soke shirin.

Masu goyon bayan a soke tsarin na NYSC a majalisar dokokin kasar, sun gabatar da hujjar cewa, ana jefa rayuwakan masu yi wa kasar hidima cikin hadari, inda da yawa daga cikinsu kan rasa rayukansu.

XS
SM
MD
LG