Sojojin Najeriya Sun Kubutar Da ‘Yan Mata 200 Da Mata 93

Une manifestation tenue dimanche 12 avril 2015 à Washington, Etats-Unis, pour réclamer la libération de 276 lycéennes enlevées un an plus tôt à Chibok au Nigéria

Sojojin Najeriya sun kubutar da wasu 'yan mata 200 da mata 93 a jiya Talata, to amma har yanzu ba a tabbatar ko wasu daga cikin wadanda aka kubutar din, dalibai 'yan matan nan ne da aka sace su shekara guda da ta gabata ba.

Mai magana da yawun Ma'aikatar Tsaron Najeriya Major-Janar Chris Olukolade, ya gaya ma wakilin wannan gidan rediyon Chris Stein cewa, an samu wadanda aka sace din a wasu sansanoni uku na wuraren da ke hannun kungiyar Boko Haram mai tsattsauran ra'ayi.

Olukolade ya ce yankin na daya daga cikin wuraren da su ka rage a hannun Boko Haram, bayan da sojoji su ka fatattaki wannan kungiya mai tsattsauran ra'ayin addinin daga wasu garuruwa da kauyukan da su ka kwace. Ya ce tuni sojoji su ka lalata sansanonin.

'Yan Boko Haram sun sace dalibai 'yan mata sama da 200 daura da kauyen Chibok da ke arewacin Najeriya a cikin watan Afirilun 2014, al'amarin da ya janyo kururuwa a fadin duniya.