Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hawa Mota Maras Matuki Ka Iya Janyo Rashin Lafiya


Google's Driverless Cars
Google's Driverless Cars

Wani nazari da jami’ar binciken ababan hawa ta Michigan tayi, wanda ta fitar a satin daya gabata, na nuna cewa mota maras matuki ka iya haddasa cutar sufuri ga wasu mutane.

Cutar sufuri dai cuta ce da wasu mutane ke kamuwa da ita alokacin da suke tafiya mai nisa kan abin hawa, alamun cutar sune kamar mura da jiri da ciwon gabobi.

Abubuwa uku da ke yawaita cutar sufuri – wato rashin mawafaka tsakanin motsi da gani, da rashin sanin inda za a dosa, da rashin iko da akalar tafiya – matsaloli ne da kan ta’azzara a motocin da ke tuka kansu.

Farfesa Micheal Sivak wanda ya jagoranci gudanar da wannan binciken yace, “sakamakon da muka samu yayi nuna kaso 6 zuwa 12 cikin ‘dari na mutanen dake amfani da mota maras matuki a Amurka, za’a iya tsammanin su da kamuwa da wannan cuta.”

Amma masu nazarin na kokarin gano hanyar da zata ‘daukewa mutanen dake zaune cikin mota maras matuki hankali, domin janye hankalinsu daga kallon hanya suna ta tunane tunane, hanyoyin kuwa sun hada da karutu, kallon talabishin da kallon wasan kwaikwayo.

XS
SM
MD
LG