Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nazarin Dalilan Karin Aure A Kano Da Jigawa


Mata, Maza, Matasa da Dattijai da ma Yara sun fito domin nuna farincikinsu a kan titin Zoo Road Kano
Mata, Maza, Matasa da Dattijai da ma Yara sun fito domin nuna farincikinsu a kan titin Zoo Road Kano

A wani nazari da akayi kan karin aure a kasar hausa cikin wannan zamani da Mallam Mohammed Hadi Musa masanin ilimin nazarin halayyar ‘dan Adam a kano yayi, wanda ya samu ra’ayoyin mutane kan karin aure a jihar Kano da Jigawa Najeriya.

Wadannan jihohi biyu dai suna ‘daya daga cikin jihohin da aka fi samun yawaitar karin aure a Najeriya, anyi nazarin ne inda aka ji dalilan da mazaje su kayi amfani wajen yanke shawarar karin aure, an kuma samu yawan mutanen da suka sa hannu cikin nazarin inda raba mutanen bisa ‘dari.

kashi arba’in da biyu 42% sunce su sun kara aure ne saboda addinin musulunci yayi musu sharadi su kara aure, kuma ba dai dai bane su zauna da mata ‘daya. Hakan yasa Mallam Hadi, ya danganta wannan lamarin da al’ada, kasancewar hakan yafi tafiya da al’ada a wannan zamani, idan aka duba ba kasafai ake duba karin aure ta ma hangar addini ba, an fi kallon sa ta kafar al’ada, duk da dai ana yinsa ne domin addini, amma anfi ganin cewa kasaita ne, girma ne, auren mata fiye da ‘daya.

Kashi biyu 2% sunce suna son yin auren mata fiye da ‘daya domin tara yawan ‘ya ‘ya dayawa.

Kashi goma sha daya cikin ‘dari 11% su kuma sunce sun kara aurene saboda matar su ta farko da suka aure ta canza, wanda hakan na faruwa ne a dalilin haihuwa da ‘kara girma, canjawar jiki da dai sauransu.

Kashi arba’in da ‘daya 41% sun ce ‘bacin rai da bakin ciki da gazawa na matar farko da suka aura shine dalilinsu na neman karin aure.

Kashi hudu cikin ‘dari 4% kuma sun nuna cewa sun kara aure ne a saboda dalilai kamar su, neman haihuwa, bukatar saduwa da mace fiye da ‘daya, sha’awa.

XS
SM
MD
LG