Akwai bukatar iyaye su bama ilimi matukar mahimanci ga ‘yayansu, neman abun duniya kada yasa iyaye su dinga mantawa da rayuwar yara manyan gobe.
Wani yaro me kimanin shekaru gomasha takwas da haihuwa, kuma dan makarantar sakandire, yana taimakama iyayenshi wajen neman abun yau da kullun. Shi dai wannan matashin yakan je makaranta bayan yadawo kokuma a ranakun da baya zuwa makaranta, yakan yi sana’ar soya wara ma mahaifiyarsa a harabar gidansu, don samun kudin kashewa ga mahaifiyar tasu da kuma biyan bukatunsu nayau da kullun.
Baya ga haka wannan matashin yakan je yayi sana’ar gini inda ma nan yakansamo kudin dayake yin lalurashi dama tallafama iyayensa. Abun lura a nan shine iyayen wanna yaron sun sashi a hanyar dai dai don iya dogaro da kanshi, batare da yayi kwanto da wani yabashi ba.
Wannan wani abune da yakamata ace kowane iyaye su nuna ma ‘yayansu hanyoyin dogaro da kai kuma babu sana’ar namiji ko ta mace idan har dai za’a samu abun magance matsalar yau da kullun.